Jagoran ‘yan wasan Manchester United Harry Maguire ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi wanda zai ba shi damar ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa watan Yuni na shekarar 2027.
Fabrizio Romano ya ruwaito cewa tsohon dan wasan na Ingila mai shekaru 33, ya kusa kammala zama a kungiyar ƙarshen a kakar ta bana amma ya amince da kulla sabuwar yarjejeniya domin ci gaba da zamansa a Manchester United.
Jaridar Punch ta ambato Maguire, wanda ya koma United daga Leicester City a shekarar 2019 kan kuɗi kusan fam miliyan 80, ya buga wasanni 266 inda ya zura kwallaye 17 a ƙungiyar.
