Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMahajjatan Kaduna sun mayar da fiye da naira Miliyan 14 da aka...

Mahajjatan Kaduna sun mayar da fiye da naira Miliyan 14 da aka manta ga masu su

Alhazan biyu daga jihar Kaduna sun mayar da kayayyaki da kudade da aka manta da su yayin aikin hajji, da darajarsu ta haura naira miliyan 14.

Shafi’u Abdul’aziz daga Lere ya samu jakar kudi da wayoyi a Harami, mallakin wani dan Mali, ya kai ta ga hukumar alhazai.

Haka kuma, Alhaji Sha’aban Sidi daga Igabi ya mika wata jaka da ya samu a bandaki, wacce ta ƙunshi kimanin naira miliyan 4, mallakin wani dan Aljeriya.

Hukumar alhazai ta Kaduna ta yaba da gaskiya da amana da alhazan suka nuna, tana mai cewa hakan abin koyi ne ga alhazai na duniya kamar yadda shafin Facebook na Hajj Reporters ya tabbatar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata