Majalisar Dattijai ta Nijeriya ta bayyana cewa ba za ta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba har sai ta karɓa kuma ta duba takardar hukuncin kotu, da ya shafi karar da ke tsakaninta da Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio.
Shugaban kwamitin hulɗa da jama’a na majalisar Sanata Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan, a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.
A ranar 6 ga Maris, 2025, Majalisar ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon wata shida bayan rikici da ya shiga tsakaninta da shugabancin majalisar kan sauya mata wurin zama.
Natasha ta garzaya kotun tarayya a Abuja, inda Mai Shari’a Binta Nyako ta umurci majalisar dattawa da ta janye dakatarwar.
Sai dai kotun ta kuma same Natasha da laifin raina kotu tare da hukunta ta da tara na naira miliyan biyar.
Adaramodu ya ce Majalisar ta riga ta nemi takardar hukuncin wato CTC tun ranar Litinin, kuma ba za ta ɗauki wani mataki ba har sai ta samu takardar don yin nazari.
Majalisa dattawa ta ce ba za ta mayar da Natasha ba har sai ta karɓi takardar hukuncin kotu
Recent Comments
on Gwamnatin Tinubu za ta fara ba da rancen maras kuɗin ruwa ga manoma da masu ƙananan sana’o’i – GEEP
on Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga yanzu zuwa shekarar 2030
on Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga yanzu zuwa shekarar 2030
on Jaridar Daily Trust ta gano dalilai uku da suka sa Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC na kasa
on Peter Obi ya sake jaddada bukatar kafa tsarin wa’adin shekara 5 kacal ga shugaban ƙasa a Najeriya
on Cire tsoffin ‘yan sanda daga daga tsarin Contributory Pension Scheme ya fi karfina – IGP Egbetokun
on Gwamnatin Nijeriya ta ɗage buɗe shafin neman aiki na Immigration, Civil Defence da sauran hukumomi
on APCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda ya zo da maciji a fadar gwamnati
on An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3
on APCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda ya zo da maciji a fadar gwamnati
on An karkatar da Naira Bilyan 71.2 daga cikin Bilyan 100 na bashin dalibai a Nijeriya – Hukumar ICPC
on Gwamna Abba Gida Gida ya zabi tsohon shugaban ma’aikatansa da wasu mutum 5 a matsayin kwamishinoni
on Nijeriya za ta zama jagorar kasuwar halal ta duniya mai jarin Dala bilyan Dubu 7 – Kashim Shettima
