By Salim Muhammad Gali
Majalisar dattawa ta Nijeriya na duba yiwuwar ƙara yawan alkalai a kotun kolin kasar daga 21 zuwa 30, domin rage yawan shari’u da ke taruwa a gaban kotun da kuma saurin yanke hukunci.
Wannan na zuwa ne bayan wani kudiri da Sanata Osita Izunaso daga Imo ta Yamma ya gabatar, yana mai bayyana cewa alkalai 21 ba su wadatar ba, duk da an nada su tun 2023.
Sanata Izunaso ya ce adadin alkalai 30 zai ba da damar kafa kwamitoci fiye da hudu a lokaci guda, wanda hakan zai taimaka wajen gudanar da shari’u cikin gaggawa.
Ya kuma yi kira da a dakatar da karɓar ƙananan shari’u a kotun koli, kamar rikicin fili, da saki, yana mai cewa irin waɗannan su rika tsayawa a kananan kotunan.
