Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMajalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta magance matsalar abinci

Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta magance matsalar abinci

Majalisar dattawan Nijeriya ta tabka zazzafar muhawara a ranar Talata, inda tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar yunwa da ake fama da ita a kasar.

Majalisar ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki matakan yaki da matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar ta hanyar zayyana wasu matakan yaki da lamarin.

Majalisar dattijai ta yi nuni da cewa, a cikin ‘yan watannin da suka gabata an samu hauhawar farashin kayan masarufi a kasar nan, lamarin da ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata