Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiMajalisar Dattawa ta dakatar da muhawara kan gyaran dokar zabe tare da...

Majalisar Dattawa ta dakatar da muhawara kan gyaran dokar zabe tare da shiga zaman sirri

Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar da muhawarar kan kudirin dokar zaɓe ta 2022, domin bai wa ’yan majalisa damar yin nazari mai zurfi kafin ɗaukar mataki na ƙarshe.

An yanke wannan shawara ne a zaman Majalisar na ranar Laraba, bayan tattaunawa kan rahoton kwamitin majalisar dattawa kan harkokin zaɓe, wanda aka gabatar ba tare da halartar shugaban kwamitin ba, Sanata Simon Lalong.

Majalisar ta amince a janye muhawarar a wannan lokaci, tare da ci gaba da duba dokar ranar Alhamis, sannan majalisar ta kuma shiga zaman sirri domin tattauna muhimman batutuwan da ke cikin kudirin, ganin irin tasirin da gyaran dokar zai iya yi ga zaɓuka masu zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata