Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMajalisar Dattawa za ta yi zama na musamman a ranar Laraba domin...

Majalisar Dattawa za ta yi zama na musamman a ranar Laraba domin girmama Marigayi Buhari

Majalisar dattawan Nijeriya ta bayyana shirinta na gudanar da zama na musamman a ranar Laraba mai zuwa domin nuna girmamawa da tunawa da marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Wannan zama na musamman zai mayar da hankali ne kan gagarumar gudunmawar da marigayin ya bayar wajen ci gaban Nijeriya, tun daga lokacin da ya hau mulki har zuwa saukarsa, kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito.

A makon da ya gabata, Majalisar Zartaswa ta Tarayya ma ta gudanar da irin wannan zama domin tunawa da rayuwa da hidimar marigayin, wanda ya rasu kwanan nan.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a yayin taron Majalisar Zartaswa, ya bayyana Buhari a matsayin shugaba wanda ya jagoranci kasar cikin gaskiya da rikon amana, yana mai cewa Buhari ya bar tarihi mai kyau da za a ci gaba da tunawa da shi a tarihin Nijeriya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata