Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaMajalisar dattawan Nijeriya ta ba shugaban NNPCL wa’adin mako 3 bayyana kan...

Majalisar dattawan Nijeriya ta ba shugaban NNPCL wa’adin mako 3 bayyana kan batan Naira tiriliyan 210

Majalisar dattawan Najeriya ta bai wa Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, wa’adin makonni uku domin ya bayyana cikakken bayani kan inda aka karkatar da Naira tiriliyan 210 daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Sanata Ahmed Wadada, shugaban kwamitin Majalisar kan lissafin kuɗin jama’a, ne ya bayyana hakan bayan zaman tattaunawa da Ojulari ranar Talata.

Wadada ya ce ba wai an sace kudaden ba ne, ko kuma sun bace, sai dai babu cikakken bayani kan yadda aka kashe su, wanda hakan ya haifar da cece-kuce daga ‘yan Majalisa da masu ruwa da tsaki a tattalin arzikin ƙasar.

Majalisar ta bukaci Ojulari ya gabatar da cikakken bayani kan dukkan tuhumar da ke cikin rahoton binciken nan da makonni uku.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata