Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da wasu mambobi biyar na kwamitinta kan kananan hukumomi, tsaro da al’amuran sarauta, bisa zargin sauya gaskiyar rahoton bincike da ya shafi shugaban karamar hukumar Otukpo, Hon. Maxwell Ogiri.
Sanarwar mai magana da yawun Kakakin Majalisar, Terver Zamber, ta bayyana cewa an dakatar da mambobin har na zaman majalisa uku saboda yunkurin kare shugaban karamar hukumar daga hukunci.
Wadanda aka dakatar sun hada da: Hon. Shimawua Terna da Hon. Mathew Damkor da Hon. Cephas Dyako da Hon. Moses Egbodo da kuma Hon. Isaac Echekliye.
Majalisar ta kafa wani sabon kwamiti na wucin gadi karkashin Hon. Ipusu domin sake nazarin zarge-zargen almundahana da rufe zauren majalisa da ake zargin shugaban Otukpo da aikatawa.
