Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiMajalisar wakilai ta umarci jami'an tsaro su kama gwamnan babban bankin kasa

Majalisar wakilai ta umarci jami’an tsaro su kama gwamnan babban bankin kasa

 Majalisar wakilan
Najeriya ta baiwa jami’an tsaro umarnin kama gwamnan babban banki CBN Mr Olayemi
Cardoso da Akanta Janar ta kasar Mrs Oluwatoyin Madein da karin wasu mutane 17,
sakamakon kin amsa gayyatar da ta yi musu a lokuta da dama.

Wannan umarni na
zuwa ne bayan bukatar hakan da dan majalisa Fred Agbedi daga jihar Bayelsa ya
mikawa majalisar.

Da yake karantowa majalisar muhimmanci kamo mutanen,
ya ce dabi’ar su ta kin girmama majalisar ya nuna irin girman kan da suke da
shi da kuma raina majalisa.

Don haka ne ya ce ya
zama dole majalisar ta yi amfani da karfin da take da shi wajen tursasa musu
gurfana a gaban ta, dalili kenan da ya sa kakakin majalisar Tajudden Abbas ya
umarci babban sufeton ‘yan sanda na kasa da ya kamo mutanen da kuma tabbatar
sun duka a gaban majalisar.

Majalisar
na bukatar su gurfana gaban ta don yi mata bayani filla-filla kan abinda zasu
yi da kudaden da aka ware musu a cikin kasafin kudin badi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata