DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabaraiMajalisar wakilai ta umurci Akanta Janar na Nijeriya ya fitar bayanan aiyukan...

Majalisar wakilai ta umurci Akanta Janar na Nijeriya ya fitar bayanan aiyukan kwangilar Niara tiriliyan 2.4 da aka amince 

Majalisar wakilan Nijeriya ta umurci Akanta Janar na kasa, Shamsudeen Ogunjimi, da ya gabatar da cikakkun bayanai kan yadda aka biya kuɗaɗen kwangila na sama da naira tiriliyan 2.4 da gwamnatin tarayya ta amince da su.

Wannan na zuwa ne bayan tabbacin da ofishin Akanta Janar ya bayar cewa gwamnati ta amince da biyan kuɗaɗen kwangilar domin aiwatar da manyan ayyuka a fadin ƙasar.

A cewar wata sanarwa da sakataren yada labarai na mataimakin kakakin majalisar, Chief Levinus Nwabughiogu, ya fitar a Abuja, majalisar ta jaddada bukatar tabbatar da sahihancin ayyukan da aka biya, tare da gargadin gujewa biyan kuɗi ga ayyukan da ba su da amfani ga ‘yan ƙasa.

Mataimakin kakakin Majalisar, Hon. Benjamin Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin da majalisar ta gudanar da wani zama da gwamnati da ‘yan kwangila a baya, ya ce an cimma matsaya bayan wata zanga-zanga da ‘yan kwangila suka yi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata