Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMajalisar wakilan Najeriya za ta binciki batan kudade a wasu ofisoshin...

Majalisar wakilan Najeriya za ta binciki batan kudade a wasu ofisoshin jakadancin kasashen ketare

Kwamitin majalisar wakilan Najeriya mai kula da harkokin ƙasashen ketare ya bayyana shirin fara gudanar da bincike kan zargin almundahanar wasu kudade da aka yi tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024.

Ana zargin batan Dala 172,000 ne da aka ware wa ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Vietnam, China da kuma Koriya ta Kudu.

Yayin da yake zantawa da jaridar Punch, shugaban kwamitin Oluwole Oke ya ce tuni aka gayyaci dukkanin masu ruwa da tsaki a lamarin don gano yadda wadannan kudade suka bace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata