Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta amfani da dukkan matakan diflomasiyya domin ganin ta dawo da tsohon shugaba Goodluck Jonathan cikin koshin lafiya daga Guinea-Bissau, inda yake makale sakamakon juyin mulkin da aka yi a ranar Laraba.
Dan majalisa Julius Ihonvbere ne ya gabatar a yayin zaman majalisar wakilan na ranar Alhamis.
A cewar Ihonvbere, Jonathan ya je Guinea-Bissau ne domin sa ido kan zaben kasar, amma ya makale lokacin da sojoji suka karbe mulki bayan lokacin sanar da sakamakon zabe ya kusa. Majalisar ta bukaci gwamnati ta yi duk mai yiwuwa domin ganin dawowarsa lafiya.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa dubban masu sa ido kan zabe daga kasashe daban-daban sun makale a filin jirgi tun ranar Laraba, bayan sojoji sun karbe ikon kasar tare da saka dokar hana fita a kasar.
