Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMajalisar wakilan Nijeriya ta wanke kasar Togo daga zargin badakalar digirin bogi

Majalisar wakilan Nijeriya ta wanke kasar Togo daga zargin badakalar digirin bogi

Majalisar wakilan Nijeriya ta wanke jamhuriyar Togo daga zargin bada shedar digirin bogi, biyo bayan cece-kuce da ya mamaye fannin ilimin kasar a kwanakin da suka gabata.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin majalisar da ke kula da koke-koken jama’a ya mayar da hankalin kan binciken jamhuriyar Benin, inda ake zargin ana bayar da jabun satifiket na digiri kamar ruwa.

Shugaban kwamitin, Bitrus Laori ne ya bayyana hakan yayin wani zaman da ya gudana a Abuja ranar Juma’a, biyo bayan korafin da wata kungiya ‘Sovereign Legal Practitioners’ suka shigar a madadin masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.

Takardar koken ta nemi yin bincike kan sanarwar da ma’aikatar ilimi ta Nijeriya ta fitar a shekarar da ta gabata, inda take zargin kasashen Togo da Jamhuriyar Benin da bayar da digirin bogi.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata