Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna makarantu da yawa a rufe suke yayin da wasu kuma suka koma sansanin ‘yan gudun hijira.
Rahoton ya bayyana akalla akwai makarantu 39 a jihar Zamfara, 30 a Jihar Niger, 6 a jihohin Kaduna da Sakkwato. Sai kuma 52 a jihar Katsina da 55 a jihar Benue.
Sai dai, binciken na Daily Trust bai sanya jihohin Borno, Adamawa da kuma Yobe ba wadanda su ma ke fama da aikace-aikacen ‘yan bindiga tsawo shekaru 15.
Wannan adadi na iya haurawa ko akasin haka sakamakon wasu wuraren ba su shiguwa kamar yadda jaridar ta Daily Trust ta ruwaito.
