Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaMalam Nasiru El-rufa’i ya jagoranci hadewar jam’iyyar SDP da ADC a Kaduna

Malam Nasiru El-rufa’i ya jagoranci hadewar jam’iyyar SDP da ADC a Kaduna

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jinjinawa abin da ya kira da hangen nesa bayan da jam’iyyar SDP ta haɗe gaba ɗaya da jam’iyyar ADC a Kaduna.

Lamarin ya faru ne a wata ganawar manyan shugabanni da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga Agusta, 2025, a Kaduna, inda El-Rufai ya jagoranci taron.

Taron ya samu halartar manyan ‘yan siyasa daga ADC, shugabannin SDP, tsofaffin kwamishinoni, da wasu daga PDP.

Jaridar Punch ta ruwaito El-Rufai ya ce wannan haɗin gwiwa babban mataki ne wajen samar da ƙarfi guda domin cimma cigaba da shugabanci nagari a jihar.

Shugaban ADC a Arewa maso Yamma, Ja’afar Mohammed Sani, ya yaba da matakin da SDP ta dauka wajen fifita bukatar jama’a a yayin shiga hadakar siyasar ta ADC a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata