Tuesday, April 7, 2026
HomeWasanniManchester City ta kammala daukar Donnarumma daga PSG

Manchester City ta kammala daukar Donnarumma daga PSG

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta tabbatar da daukar sabon mai tsaron raga, Gianluigi Donnarumma, daga PSG a ranar Talata kan kuɗin da ya kai kusan Yuro miliyan 35.

Donnarumma mai shekaru 26, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyar, daidai lokacin da tsohon mai tsaron ragar Man City Ederson ya koma Fenerbahçe bayan shekaru takwas da ya shafe a kungiyar ta City.

Tsohon mai tsaron ragar na Milan ya taba lashe gasar Champions League tare da PSG, kuma shi ne ya tsare wa tawagar Italiya raga lokacin da ta lashe gasar Euro 2020.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata