Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Alkalin babbar kotun jihar Bayelsa, Justice E.G. Umokoro, da misalin karfe 7:30 na daren Asabar a unguwar Ekeki, kusa da wani gidan cin abinci.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sanye da bakaken kaya ne suka zo dauke da bindigu, inda suka tare motar Alkalin da wata Hilux marar lamba suka kuma tafi da shi bayan harbe-harbe.
Rahoton Jaridar Daily Trust ya bayyana cewa an ga bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, na nuna yadda Justice Umokoro ke kokarin tserewa kafin a tilasta masa shiga motar masu garkuwar.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Bayelsa, DSP Musa Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’an tsaro da na’urorin leken asiri (drone) domin gano inda aka kai Alkalin da kuma cafke wadanda ke da hannu cikin satar.
