Mataimakiyar Firaministan Burtaniya Angela Rayner ta sanar da yin murabus daga mukaminta, bayan da wani bincike ya gano cewa ta karya ka’idojin shugabancin gwamnati.
Tun da fari dai Rayner ta amince da cewa ba ta biya cikakken harajin wata kadara da ta saya ba, inda ta tuntubi mai bai wa gwamnati shawara kan dokokin shugabanci, kamar yadda jaridar punch ta wallafa.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa mataimakiyar Firaministan ba ta dauki shawarar da aka ba ta ba, lamarin da ya jawo murabus din ta, domin kare martaba da kimar iyalin ta, kamar yadda ta bayyana cikin wata wasika da ta aikewa Firaministan.
Sir Keir Starmer ya bayyana bakin cikin rasa ta a cikin gwamnati, sai dai ya ce za ta ci gaba da kasancewa babbar jigo a jam’iyyar su ta Labour.
