Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaMatakan da Shugaba Tinubu ke dauka sun taimaka wajen rage talauci a...

Matakan da Shugaba Tinubu ke dauka sun taimaka wajen rage talauci a Arewacin Nijeriya – Gwamna Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya bayyana cewa babu wata gwamnati a tarihin Nijeriya da ta zuba jari a harkar noma kamar yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi cikin shekaru biyu da suka gabata.

Gwamna Uba Sani ya ce matakan da Tinubu ya dauka sun taimaka matuka wajen rage talauci a Arewacin kasar.

Uba Sani ya jaddada irin goyon bayan da ake bai wa kananan manoma, tallafin takin zamani, da kuma taimakon kudi ba tare da la’akari da jam’iyya ba ga jihohi.

Ya danganta wadannan kokari da cike gibin ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi, da kuma rage talauci a cikin al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata