Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMatan da aka sace a Neja sun dawo da juna biyu da...

Matan da aka sace a Neja sun dawo da juna biyu da jarirai bayan shekara ɗaya a hannun ‘yan ta’adda

Wasu daga cikin mata da aka sace a ƙananan hukumomin Rafi da Shiroro na Jihar Neja tun a watan Fabrairu 2024 sun dawo gida daga hannun ‘yan ta’adda, inda da dama daga cikinsu ke da juna biyu ko kuma suka dawo da jarirai.

Rahotanni sun nuna cewa ciki juna biyu da jariran da matan ke ɗauke da su na ‘yan ta’addan da suka tsare su fiye da shekara guda ne, kafin jami’an ‘yan sanda su ceto su makonni baya.

Daily Trust ta ruwaito cewar an gano cewa huɗu daga cikin matan suna cikin mutum 25 da aka sace a kauyen Allawa, a kan hanyar Pandogari-Allawa, yayin da suke dawowa daga kasuwa a watan Fabrairu 2024.

Wasu rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun ɗauko matan da yawansu ya kai 24 daga Palu-Waya a karamar hukumar Shiroro a cikin motocin haya, suna ƙoƙarin mayar da su wani wuri daban.

Amma da suka iso yankin Kagara a karamar hukumar Rafi, wata daga cikin matan ta nemi izinin yin lalura. Lokacin da aka tsaya, sai ta ankarar da jama’a tare da neman taimako wanda hakan ya jawo hankalin jama’a, kuma hakan ne yasa aka ceto su daga hannun barayin da kuma cafke direban da yanzu ke hannun ‘yan sanda.

Wata majiya daga hedikwatar ‘yan sandan Jihar Neja da ke Minna ta tabbatar da cewa a yanzu haka matan na karkashin kulawar rundunar, kuma an gano makamai a cikin jakar ɗaya daga cikin matan.

Haka kuma, majiyar ta tabbatar cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto tana cikin ‘yan matan Chibok da aka dade ana nema, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata