Mamaki ya mamaye zukatan mutanen unguwar Madina UN da ke birnin Accra na kasar Ghana bayan wata mata da ake zaton ta mutu yayin aikin Hajjin bana, 2025 ta dawo gida da rai, kwanaki bayan iyalanta sun riga sun yi mata jana’iza.
Matar, mai suna Fatima Kassim, an rawaito cewa ta rasu a Saudiyya, tare da takardar mutuwa da ofishin jakadancin Ghana ya fitar da ta tabbatar da rasuwar. Bisa wannan takarda ta hukuma, danginta masu jimamin rasuwarta suka shirya mata jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.
Sai dai abin mamaki, Fatima ta iso gida da yammacin ranar Laraba, 2 ga Yuli, abin da ya bar mazauna yankin cikin ruɗani da firgici. Wasu daga cikin makwabta ma sun gudu suna tunanin fatalwa suka gani.
Da suke zantawa da Citi News a gidan dangin Fatima da ke Madina, ’yan’uwanta sun bayyana farin cikinsu da kuma dimautarsu da wannan al’amarin.
