Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiMatasa a Kano sun lahanta ofishin ‘yansanda kan mutuwar wani da ake...

Matasa a Kano sun lahanta ofishin ‘yansanda kan mutuwar wani da ake zargi a caji ofis

A ranar Litinin ne wasu matasa suka kona wani bangare na ofishin ‘Yansandan da ke Rano a jihar Kano bayan mutuwar wani Abdullahi Musa da ake zargi a caji ofis.

An kama Abdullahi Musa ne a ranar Lahadi bisa zargin aikata laifin karya dokar amfani da hanya.

Dalilin haka ne wasu fusatattun matasa suka fito zanga-zangar lumana inda daga bisani abin ya canza salo sakamakon halbi da ‘yansandan suka yi cikin masu zanga-zangar, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane 2, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wani bangare na ofishin ‘Yansandan ne masu zanga-zangar suka lahanta.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata