Wani faifan bidiyo da ya karade shafukan yanar gizo, ya nuna yadda wani matashi mai suna Gbenga ya rasa ransa sakamakon shiga gasar daukar buhun siminti da yawa a kansa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa matashin ya shiga jerin masu son nuna bajinta tsakanin abokansa ne, inda suka sanya gasar daukar buhun siminti biyar a kai.
Jaridar ta kuma ce da fari matashin ya dauki buhuna 4 kafin daga baya ya fadi kasa warwas, inda nan take da daina motsi.
An dai saka musu gasar ne da nufin bayar da kyautar waya da duk wanda ya lashe.
