Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMatatar Dangote ta shigo da danyen mai ganga miliyan 3.65 cikin watanni...

Matatar Dangote ta shigo da danyen mai ganga miliyan 3.65 cikin watanni biyu – Jaridar Punch

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce matatarsa ta fara dogaro da Amurka wajen samun danyen mai saboda ba ta samu isasshe a nan cikin gidan

Dangote ya bayyana haka ne a lokacin da ko’odinetar kwamitin kula da cinikin danyen mai da kudin Naira na Shugaba Tinubu, Maureen Ogbonna, ta jagoranci wata tawaga zuwa matatar.

Aliko Dangote ya yabawa kwamitin kan rawar da suke takawa wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar canjin danyen man fetur da kudin Naira, sai dai ya ce saboda karancin danyen mai a cikin gida, matatar na kara dogaro da shigo da shi daga Amurka don biyan bukatunta a cikin ‘yan watannin nan.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da binciken jaridar Punch ta yi hasashen cewa matatar man Dangote za ta shigo da jimillar gangar danyen mai miliyan 17.65 tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin 2025, inda tuni ya shigo da kusan ganga miliyan 3.65 a cikin watanni biyun da suka gabata.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata