Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMatsalar tsaro ta ragu a karkashin mulkin Tinubu a Arewa ta tsakiyar...

Matsalar tsaro ta ragu a karkashin mulkin Tinubu a Arewa ta tsakiyar Nijeriya – APC Forum

Ƙungiyar APC North-Central Forum ta zargi tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da yaɗa ƙarya da farfaganda kan tsaron Arewa ta tsakiyar Nijeriya.

El-Rufai ya yi zargin cewa matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara a yankin karkashin mulkin Shugaba Bola Tinubu, tare da ikirarin cewa gwamnatin tana biyan kuɗi ga ’yan ta’adda.

Sai dai a martanin da ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar APC Forum ƙarƙashin jagorancin Alhaji Saleh Zazzaga ta ce sabanin zargin El-Rufai, gwamnatin Tinubu ta rage matsalar tsaro a yankin tun bayan da ta karɓi mulki a 2023.

Ya ce matsalar tsaro yanzu ta ragu idan aka kwatanta da lokacin baya, a da manoma ba sa iya zuwa gona saboda tsoron hare-hare, amma yanzu suna iya zuwa gonakinsu saboda umarnin da Shugaba Tinubu ya bai wa jami’an tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata