Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiMatsalar tsaron Arewa maso Yamma ba irin na Arewa maso Gabas ne...

Matsalar tsaron Arewa maso Yamma ba irin na Arewa maso Gabas ne ba – Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kalubalanci tsarin dogaro da makamai kawai wajen yakar matsalar tsaro, yana mai jaddada cewa ba a haka za a magance lamarin.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da littafin “Where I Stand” na marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, wanda Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara zuwa harshen Larabci.

Yayin jawabin nasa, Sani ya ce matsalar tsaro a arewa maso yamma ta bambanta da ta Boko Haram a arewa maso gabas wacce ta samo asali daga akida. Ya jaddada cewa talauci, rashin aikin yi da kuma mantawa da al’ummomin karkara sune tushen ayyukan ’yan bindiga.

Gwamnan ya kuma yi nuni da cewa, duk da yawan al’ummar Najeriya da ya ninka sosai cikin shekaru 45 da suka gabata, adadin jami’an tsaro bai karu yadda ya kamata ba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata