Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMe faduwar jam'iyar ADC a zaben cike gurbi ke nufi ga nasararta...

Me faduwar jam’iyar ADC a zaben cike gurbi ke nufi ga nasararta a 2027?

Jam’iyya mai mulki wato APC ce ta fi rinjaye inda ta lashe kujeru 12, sai PDP da ta samu nasara a Ibadan din jihar Oyo yayin da NNPP tayi nasara a Kano, sannan APGA ta lashe mazabu biyu a Jihar Anambra.

Biyo bayan hakanne yasa jam’iyyar ADC bayyana rashin jin dadin ta da yadda aka gudanar da zaben, tana zargin cewa an yi amfani da barazana da cin hanci a lokacin gudanar da zabukan.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar ta ADC na kasa Bolaji Abdullahi ya fitar yace zaben cike ya ke da magudi ta hanyar sayan kuri’u da tashe-tashen hankula.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata