Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMiji ya saki matarsa a Caji Ofis bayan 'yansanda sun kama ta...

Miji ya saki matarsa a Caji Ofis bayan ‘yansanda sun kama ta a wani a samamen Otel a Minna

Wani mutum a Minna, Jihar Neja, ya saki matarsa a cikin caji ofis bayan jami’an tsaro sun cafke ta a wani samame da aka kai otal, inda ake zargin ‘yan sara-suka da masu safarar miyagun kwayoyi ke buya.

Wata majiya daga cikin jami’an tsaron ta shaidawa Daily Trust cewa matar na cikin wadanda aka kama yayin da aka kai farmaki otal-otal da ake kyautata zaton su ne mafakar bata-gari da masu shaye-shaye a cikin birnin Minna.

A cewarsa, asalin matsayin matar a matsayin wadda ke da aure bai bayyana ba sai bayan an kaisu caji ofis, sannan ‘yan uwanta da na wasu daga cikin wadanda aka kama suka iso.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata