Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBa gwamnatin Nijeriya ta ba ƴan matan da suka lashe gasar Turanci...

Ba gwamnatin Nijeriya ta ba ƴan matan da suka lashe gasar Turanci kyautar ₦200,000 ba

Ma’aikatar ilimi ta Najeriya ta bayyana cewa Minista Tunji Alausa ne ya ba ƴan matan Yobe da suka lashe gasar Turanci kyautar ₦200,000, ba gwamnatin tarayya ba.

Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ce ta jaddada hakan, inda ta ce ministan ya bayar da kyautar ne kawai don karfafa gwiwar sauran dalibai wajen mayar da hankali kan karatu.

Sanarwar da aka fitar a ranar 3 ga watan Satumban 2025, ta kuma ce ba a ware wa ma’aikatar wani kasafi don bayar da kyautar ga kowane dalibi a Najeriya ba.

A ranar 28 ga watan Agustan 2025 ne dai aka gabatar da bikin jinjinawa daliban da suka samu nasara a gasar TeenEagle da ta gudanar a kasar Birtaniya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata