Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMinistan Abuja Nyesom Wike ya ba da umarnin rufe asibitocin da aka...

Ministan Abuja Nyesom Wike ya ba da umarnin rufe asibitocin da aka yisu ba bisa ka’ida ba

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba da umurnin rufe duk wani asibitin da ba a yi wa rajista ba da kuma ma’aikatan jinya da ke aiki a babban birnin tarayya Abuja.

Babban mataimaki na musamman ga ministan kan harkokin yada labarai Olayinka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Asabar.

Olayinka ya bayyana cewa ministan ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake magana kan mutuwar wata mata mai juna biyu a wani asibiti mai zaman kansa da ke Durumi, Abuja, bayan tiyatar da aka yi mata.

A cewarsa, ministan ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana gudanar da aikin ta haramtacciyar hanya ko kuma yana aiki a wani asibiti da bashi da rajista to a kama shi kuma a hukunta shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata