Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaMKO Abiola ne ya lashe zaben ranar 12 ga watan Yuni -...

MKO Abiola ne ya lashe zaben ranar 12 ga watan Yuni – IBB

 

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce marigayi Basorun Moshood Kashimawo Olawale Abiola ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

IBB ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “A Journey in Service” wanda aka kaddamar a Abuja ranar Alhamis.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo wanda ya duba littafin ya ruwaito Babangida na cewa Marigayi MKO Abiola ne ya samu rinjayen kuri’u a lokacin zaben.

Idan zaku tuna abaya dai tsohun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama Abiola da lambar girma ta GCFR.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata