Sunday, April 5, 2026
HomeWasanniMorocco na dab da zama kasar Afrika ta farko da ta samu...

Morocco na dab da zama kasar Afrika ta farko da ta samu cancantar zuwa gasar cin kofin duniya na 2026

Ƙasar Morocco na kan gaba wajen samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026, inda ake sa ran za ta zama ta farko daga Afrika da ta samu gurbi a gasar.

Tawagar ƙasar da Achraf Hakimi, ɗan wasan PSG kuma ɗan takara a kyautar zama zakaran dan kwallon duniya “Ballon d’Or ke jagoranta, za ta samu tabbacin gurbi idan ta doke kasar Niger,wannan zai ba ta damar samun maki mai yawa a Group E, muddin Tanzania ba ta yi nasara a kasar Congo Brazzaville a ranar kafin wasan ba.

Morocco na jan ragamar teburi da maki 15 daga wasa 5, yayin da Tanzania ke da maki 9, Zambia da Niger na da 6 kowanne, sai Congo da ba ta samu ko maki guda ba saboda matsalolin gudanarwa.

Idan Morocco ta doke Niger, wasan da za ta buga da Zambia a ranar 8 ga Satumba a Ndola na iya zama na tabbatar da samun tikitin shiga gasar, inda za ta bukaci maki daya kacal.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata