Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMun dauki alhakin faduwar jirgin fasinjan Kaduna zuwa Abuja - Hukumar NRC

Mun dauki alhakin faduwar jirgin fasinjan Kaduna zuwa Abuja – Hukumar NRC

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya bayyana cewa ya ɗauki cikakken alhakin hatsarin da ya rutsa da jirgin fasinjan Abuja zuwa Kaduna a ranar Talata.

Shugaban ya ce hatsarin bai yi sanadiyyar mutuwar wani ba, abin da ya kira “rufin asirin Allah” domin irin wannan haɗari kan munana a wasu lokutan.

Duk da haka, ya tabbatar da cewa mutane huɗu daga cikin fasinjoji sun samu mummunan rauni, yayin da wasu biyu aka sallame su daga asibiti nan take.

Opeifa ya bayyana cewa hatsarin bai kamata ya faru ba, kuma NRC za ta tabbatar da cewa irin haka ba zai sake faruwa ba.

A yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, ya ce Yanzu haka sun dakatar da hanyar Warri-Itakpe makonni uku da suka gabata saboda tsaro, inda ake yin gyaran manyan layin jirgin domin gujewa irin wannan matsala.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata