Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiMun kama 'yan ta'adda 450 da ceto mutane 180 da aka yi...

Mun kama ‘yan ta’adda 450 da ceto mutane 180 da aka yi garkuwa da su a Satumban 2025 – Hedikwatar tsaron Najeriya

Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ta kama ‘yan ta’adda akalla 450, tare da ceto mutane 180 da aka yi garkuwa da su a cikin watan Satumban 2025.

Daraktan yada labaran rundunar Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a ranar Asabar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewar sa, ‘yan ta’adda 39 sun zubar da makamansu tare da mika wuya ga jami’an soji, baya ga samun nasarar kwato tarin manyan makamai da alburusai a watan.

Kangye ya ce sojojin sun samu wannan gagarumar nasara ce karkashin shirye-shiryen hadin gwiwa da suka hadar da ‘Operation Hadin Kai’, ‘Operation Fansan Yamma’, ‘Operation Whirl Stroke’ ‘Operation Delta Safe’ da kuma ‘Operation Udo Ka’.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata