Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaMun magance sabaninmu, yanzu a shirye nake nayi aiki da Fubara -...

Mun magance sabaninmu, yanzu a shirye nake nayi aiki da Fubara – Nyesome Wike

Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya bayyana cewa rikicin siyasa tsakaninsa da tsohon yaronsa ya kawo karshe kuma zaman lafiya ya dawo a jihar Rivers.

Wike ya ce shi da dakataccen gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da ‘yan majalisar dokokin jihar sun sasanta rashin jituwar da ke tsakaninsu.

Ya bayyana hakan ne biyo bayan wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu yayi da bangarorin a fadar shugaban kasa da ke Abuja a daren Alhamis.

Wike da Fubara dai sun dade suna takun saka a rikicin da ya barke a yankin Rivers, lamarin da ya taba majalisar dokokin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata