Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMun raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624 -...

Mun raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624 – Asusun NELFUND

Asusun ba da bashin karatu ga ɗaliban manyan makarantu ya bayyana cewa ya raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624, tun bayan ƙaddamar da tsarin neman bashin a watan Mayu, 2024.

Kamar yadda rahoton da Asusun ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, 28 ga Oktoba, 2025, ya nuna, an karɓi buƙatu fiye da 929,000, inda ɗalibai 624,535 suka amfana, yayin da aka samu ƙarin sabbin masu neman bashi 12,398 a rahoton baya-bayan nan.

Asusun ya bayyana cewa an biya makarantu 239 Naira biliyan 65.3 a matsayin kuɗin karatu, yayin da Naira biliyan 51.1 ta shiga hannun Ɗalibai domin ciyarwa da sauran bukatun yau da kullum.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata