Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar na binciken gwamnoni 18 da ke kan mulki a halin yanzu.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a Lagos yayin wani shirin wayar da kai kan illar lalata da wulakanta takardun kudi.
A cewarsa, EFCC na gudanar da bincike tun kafin gwamnonin su kammala wa’adinsu, kuma zata dauki matakin doka da zarar sun bar ofis.
Ya kuma bada misalin wani tsohon gwamna da EFCC ta bincika, wanda ya gudu zuwa Burtaniya bayan ya mika mulki, inda aka kama shi yana watsar da kudin fam a wani otel yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.
Shugaban EFCC ya ce wannan wani misali ne na irin almubazzaranci da rashin da’a da ake fama da shi, yana mai jaddada cewa hukumar zata ci gaba da dakile rashawa da barna a duk matakin Gwamnati kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
