Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMuna da hujja ba a makance muke goyon Tinubu ba - Kungiyar...

Muna da hujja ba a makance muke goyon Tinubu ba – Kungiyar Disciples of Jagaban

Kungiyar magoya bayan shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ta Disciples of Jagaban ta ce ba a makance ta ke nuna goyon baya ga shugaban ba, domin kuwa ta na da hujjoji.

Cikin wata sanarwa da da shugaban kungiyar na kasa Abdulhakeem Adwgoke Alawuje ya fitar, kungiyar ta bayyana cewa ta fara goyon bayan Bola Tinubu ne tun zamanin baya, a lokacin da yake rainon kudirinsa na zama shugaban Nijeriya.

Kungiyar ta DOJ, ta kafa hujjoji da cewa tana nuna goyon baya ne bisa tsare tsaren Tinubu kan tattalin arziki, musamman cire tallafin man fetur mai cike da zargin damfara.

Ta kuma bukaci yan Nijeriya su yi watsi da duk wani shiri da yan adawa ke yi da sunan hadakar jam’iyyu, domin a cewar ta yunkuri ne kawai na lalata kyakkyawan shirin da Tinubu ya yi wa Nijeriya da al’ummarta.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata