Kasashen Bénin da Côte d’Ivoire sun maida martani ga shugaba Tiani na Nijar kan zargin da yi musu na tallafawa ‘yan ta’addar da suka kai hari filin jirgin saman Diori Hamani a Yamai
Kasar Benin ce a baya bayan nan ta yi martanin a game da zargin na Tiani a kan shugaban ta Patrice Talon wanda kakakin gwamnatin kasar Wilfried Léandre Houngbédji ya ce Bénin kasa ce da ke cigaba da jan hankali masu zuba jari da masu ziyara sakamakon karfin tattalin arzikin ta da na ma’aikatun ta, dan haka ya ce kasar ba za ta taba bari ba a ci mutuncinta ba ta hanyar wasu zarge.
Ita ma kasar Côte d’Ivoire ta maida martani a game da zargin Tianin inda ministar harkokin wajen kasar ta kirayi jakadiyar Nijar a kasar domin neman bada bahasi akan kalaman na shugaba Tiani
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar ya zargi shugaban Faransa Emmanuel Macron da Patrice Talon da kuma Alassan Ouattara da tallafawa ma ‘yan ta’addar da suka kai hari filin jirgin saman Diori Hamani a yayin da yake tsokaci a gaban manema labarai lokacin da ya ziyararci inda aka kai hari

