Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaMuna maraba da Gwamna Abba a APC kuma za mu warware batun...

Muna maraba da Gwamna Abba a APC kuma za mu warware batun tikitin takara na ba hamayya kafin zabe – Abdullahi Abbas

Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas Sanusi, ya ce jam’iyyar na maraba da murabus din Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP da kuma shirin shigarsa APC, yana mai cewa siyasa wasa ne na adadi, kuma kowane kari yana ƙara wa jam’iyya ƙarfi a zaɓe. Ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya jaddada cewa APC a shirye take ta karɓi duk wanda ya ga alherin jam’iyyar ya yanke shawarar shigowa.

Dangane da rade-radin tikitin kai-tsaye ga gwamnan, Abbas Sanusi ya ce ba batun da jam’iyyar ke duba a yanzu ba ne. Ya bayyana cewa Gwamna Yusuf ba shi kaɗai zai shigo APC ba, akwai shugabannin ƙananan hukumomi, kansiloli da sauran masu riƙe da muƙamai da za su biyo shi. Ya ce bayan kammala dukkan matakan sauya sheƙa ne jam’iyyar za ta zauna ta tsara yadda za a tafiyar da al’amura domin cin nasara a zaɓen 2027, tare da guje wa rikici tsakanin tsofaffin mambobi da sababbi.

Kan jinkirin shigowar gwamnan, shugaban APC na Kano ya ce duk labaran da ake yadawa tun baya jita-jita ne kawai, domin sauya sheƙar gwamna na buƙatar manyan shawarwari da bin tsari. Ya shawarci mambobin APC da masu shigowa su fifita nasarar jam’iyya, tare da zaman lafiya da haɗin kai, yana mai cewa iko daga Allah yake, kuma APC na da kudirin gyara kura-kuran da ke addabar ƙasa domin ‘yan Nijeriya su samu sauƙi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata