Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMuna neman a bai wa jami'an mu iznin rike makamai a bakin...

Muna neman a bai wa jami’an mu iznin rike makamai a bakin aiki – FRSC

Shugaban hukumar kiyaye haddura ta Nijeriya (FRSC), Shehu Mohammed, ya bayyana cewa bai ga wata hanya ta tabbatar da doka a titunan Najeriya ba face jami’ansa su samu izinin ɗaukar makamai.

Yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin na ARISE a ranar Alhamis, Mohammed ya ce jami’an FRSC na fuskantar barazana musamman idan suna tinkarar manyan motocin dakon kaya da ke ɗauke da fasinjoji sama da kima.

Jaridar Daily Trust ta ambato shi dangane da zargin cin hanci da wasu jami’an hukumar ke yi, Mohammed ya amince da hakan, amma ya jaddada cewa FRSC ta fi sauran hukumomi tsauri wajen hukunta jami’an da aka samu da laifi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata