Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMuna neman dauki kan yawan harin da dorinar ruwa ke kawo mana...

Muna neman dauki kan yawan harin da dorinar ruwa ke kawo mana – Dan majalisar tarayya a Gombe

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Yamaltu/Deba a Jihar Gombe, Inuwa Garba, ya roki gwamnatin tarayya su kawo musu dauki kan hare-haren dorinar ruwa da suka addabi mazauna yankinsa.

Garba ya gabatar da wannan bukata ne a zaman da mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu ya jagoranta, inda ya bayyana cewa hare-haren sun yi sanadin rasa rayukan wasu mafarauta da manoma a bakin koguna da gonaki.

Ya kara da cewa, hare-haren da ke faruwa a yankin sun haifar da tsoro da tashin hankali, abin da ya tilasta wasu manoma da masu kamun kifi barin aikinsu, lamarin kuma na kara ta’azzara talauci da rashin abinci.

A ranar 5 ga watan Oktoba, wata dorinar ruwa ta afkawa masunta a cikin kwale-kwale, inda ta kashe mutum daya mai suna Yahaya Bawa, ta kuma jikkata wasu da dama kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata