Akalla mutane shida sun rasu, yayin da wasu uku suka ɓace a hatsarin kwale-kwale da ya auku a Garin Faji, karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto.
Lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis, 21 ga watan Agusta, lokacin da mazauna yankin ke tserewa daga farmakin da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai.
Kwana shida kafin wannan, mutane huɗu sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Goronyo.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu shaidu sun bayyana yadda mazauna yankin ke kwana a daji saboda tsoro, sannan su dawo gida da safe.
Ɗan majalisar dokokin jihar, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura motocin yaki kirar APC don ƙarfafa tsaro, tare da cafke wasu ‘yan bindiga huɗu kwanaki biyu da suka gabata.
Hukumar agajin gaggawa ta jihar Sokoto, SEMA ta bayyana cewa an ceto mutane 19, ana ci gaba da neman waɗanda suka ɓace tare da haɗin gwiwar NEMA, NIWA da kuma Red Cross.
