Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMutane huɗu sun tsira daga hatsarin jirgi a jihar Imo

Mutane huɗu sun tsira daga hatsarin jirgi a jihar Imo

Mutane huɗu sun tsira daga hatsarin jirgin Cessna 172 na kamfanin Skypower Express da ya yi saukar gaggawa (crash-landing) a Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe da ke Owerri, Jihar Imo, da yammacin Talata.

Hukumar Nigerian Safety Investigation Bureau (NSIB) ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 6:58 na yamma yayin da jirgin ke kokarin sauka a kan hanyar tashi da saukar jirgi (Runway 17).

Jirgin mai lambar rajista 5N-ASR na kan hanyarsa ne daga Kaduna zuwa Port Harcourt kafin matukan jirgin su yi gaggawar shawarar karkata zuwa Owerri.

Hukumar kiyaye afkuwar hadduran ta bayyana cewa jami’an tsaro da na agajin gaggawa na filin jirgin sun kai dauki cikin hanzari, inda aka ceto dukkan mutanen da ke cikin jirgin, ba tare da tashin wuta ba.

Rahoton ya ce biyu daga cikin matukan jirgin suna cikin koshin lafiya, yayin da sauran biyun da suka suma tun farko aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata