Mutum uku sun rasa rayukansu bayan wani mutum ya farmake su da wuka a harabar wani masallaci da ke Kado Bimko, Unguwar 1st Avenue, Gwarinpa a Abuja, yayin da suke jiran sallar asuba.
Shaidu sun ce wanda ake zargi, Laminde Boka, ya fara lahanta wani dattijo da ake kira Alhaji Wanzam da wuka yayin da yake tsaftace masallacin da sassafe.
Daga nan ya sake farmaki wani mutum da ya yi yunkurin tare shi, wanda ya mutu a kan hanyarsa ta zuwa asibiti. Mutum na uku ma ya rasu nan take bayan da wanda ake zargin ya riske shi ya fadi.
Rahotanni sun ce jama’a sun farmaki wanda ake zargin da duwatsu da sanduna, lamarin da ya jawo mutuwarsa na take.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Dagacin Kado Bimko, Malam Ibrahim Isiaku, ya ce an rufe masallacin na wani lokaci bayan lamarin, tare da yanke shawarar hana kowa kwana a harabar masallacin nan gaba.
Yayin da rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin.
