Ministan Lafiya na Nijeriya, Farfesa Mohammed Ali Pate, ya bayyana cewa ma’aikatarsa ba ta iya aiwatar da kasafin ci gaban lafiya na shekarar 2025 ba, sakamakon sakin ₦36 miliyan kacal daga cikin ₦218 biliyan da aka ware wa bangaren.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin zaman kare kasafin kudin 2026 a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Kula da Lafiya.
Ya ce duk da cewa an saki kasafin albashi gaba ɗaya, bangaren kasafin manyan aiyuka bai samu isasshen kudi ba, lamarin da ya danganta da tsarin tsara sakin kudi daga kasa zuwa sama da ofishin Akanta Janar na Tarayya ke amfani da shi.
Jaridar Daily Trust ta ambato Farfesa Pate ya kuma shaida wa ‘yan majalisar cewa ma’aikatar ta kasa samun wasu kudaden hadin gwiwa saboda jinkirin sakin gudunmuwar Nijeriya, wanda hakan ya janyo tsaiko wajen aiwatar da kasafinta na 2025.
