Monday, April 6, 2026
HomeKetareNajeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro

Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro

Najeriya da Masarautar Saudiyya sun kulla sabuwar yarjejeniya ta shekaru biyar domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da dangantakar soja tsakanin kasashen biyu.

A cewar wata sanarwa daga Ofishin Sakataran Yaɗa Labarai na Ministan Tsaron kasar, Ahmed Dan Wudil, yarjejeniyar za ta haɗa da musayar bayanan leken asiri, horaswar soja, ƙera kayan tsaro, da haɗin gwiwa a fagen ayyukan tsaro domin bunƙasa zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Karamin Ministan Tsaron Nijeriya, Mohammed Matawalle, ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Dr Khaleed H. Al-Biyari ya wakilci Saudiyya.

Sanarwar ta ce wannan mataki babban ci gaba ne wajen ƙarfafa hulɗa, inganta haɗin kai da kuma yaki da sabbin kalubalen tsaro dake tasowa a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata