Jamiu Abiola, ɗan marigayi MKO Abiola, ya ce Najeriya da ta ci gaba matuƙa da ace an bar mahaifinsa ya hau mulki bayan nasarar zaɓen 1993.
A wata hira da Channels TV, Jamiu ya bayyana cewa soke zaɓen ya hana ƙasar amfana da bunƙasar tattalin arzikin duniya a wancan lokaci.
Jamiu, wanda ke ba Shugaba Tinubu shawara, ya koka da yadda ake ƙoƙarin mantar da rawar mahaifinsa a tarihin Najeriya, inda ya ce ya rubuta littafin Shugaban Da Bai Taɓa Mulki Ba don kare sunansa.
A 2018 ne Buhari ya karrama MKO da lambar GCFR tare da ayyana 12 ga Yuni a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya.
