Ministan Noma na Nijeriya, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa Najeriya na kashe sama da Dalar Amurka biliyan 10 a kowace shekara wajen shigo da kayayyakin abinci kamar shinkafa, alkama, sukari, kifi da ma tumatir.
Sanata Kyari ya bayyana hakan ne a Taron Noma da Fitar da Kayayyaki na First Bank 2025 da aka gudanar a Legas ranar Talata.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito ministan na nuna damuwa da matsalar shigo da kayan abinci, inda ya ce ya zama wajibi a kara zuba jari da tallafi ga manoma don bunkasa harkar noman cikin gida da kuma habaka fitar da kayayyakin gona zuwa kasashen waje.
A cewarsa, duk da cewa noman Najeriya na bada gudunmawar kashi 35% ga GDP tare da daukar kashi 35% na ma’aikata a fannin aikin gona, har yanzu kasar na samun kasa da Dala miliyan 400 daga fitar da kayan gona.
